Fitaccen jarumin fina-finan Nollywood, Zubby Michael, ya gudanar da bikin zagayowar ranar haihuwarsa a wani kulob a Legas a ranar Lahadi inda ya kashe sama da Naira miliyan 8.
Bikin da tauraro ya samu halartar taurarin Nollywood da mawakan kade-kade, kamar yadda aka gani a faifan bidiyo da hotunan da jarumin ya watsa a shafinsa na Instagram.
Jaruman socialites da na Nollywood a wajen taron sun hada da Kanayo O. Kanayo, Alex Ekubo, Ini Edo, Yul Edochie, E-money, Cubana Chief Priest, Uche Jombo, da dai sauransu.
Taurarin mawakan da suka halarci bikin sun hada da Davido, Olamide, Phyno, Portable, KCee, Rudeboy, da dai sauransu.
Zubby Michael, wanda ya cika sabuwar shekara a ranar Talata, ya karbi fili a Abuja a matsayin kyautar ranar haihuwarsa.