Kamfanin jiragen kasa na Najeriya (NRC) a ranar Alhamis, ya sanar da jinkirta aikin jirgin kasa daga Legas zuwa Kano da aka shirya yi tun farko ci gaba a ranar 13 ga Agusta saboda lalacewar layin dogo.
Fidet Okhiria, Manajan Darakta na NRC, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka ba Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Legas ranar Alhamis.
Fidet ya ce lalacewar layin dogo ya faru ne sakamakon ruwan sama a kusa da Power Line, Oshogbo, Osun, a cikin makon. Ya kuma lura cewa wata tawagar kwararru daga NRC sun yi tattaki zuwa wurin, kuma suna aiki ba dare ba rana don maido da hanyar da ta lalace.
Manajin Darakta na NRC ya kuma kara da cewa nan ba da dadewa ba za a sanar da sabon ranar da za a dawo da aikin jirgin kasa daga Legas zuwa Kano.
Sanarwar ta ce, hukumar ta NRC ta yi nadamar rashin jin dadin da jinkirin zai haifar ga fasinjoji da kwastomomi.
(NAN)